Sojojin Amurka Sun kai Hari Najeriya, Trump Ya Fadi Wanda aka Kashe

Sojojin Amurka Sun kai Hari Najeriya, Trump Ya Fadi Wanda aka Kashe

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an kashe Abu-Bilal al-Minuki, wani babban jigo a kungiyar a wani samame na hadin gwiwa tsakanin dakarun AmurkaDonald Trump ya rubuta cewa an kashe Abu-Bilal al-Minuki a Najeriya yayin wani samame na hadin gwiwa da ya hada dakarun Amurka da na NajeriyaTrump ya ce al-Minuki shi ne mataimakin shugaban kungiyar IS na biyu a duniya baki daya kuma kashe shi zai kawo karshen hare-harensa a yankuna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa sojojin kasar shi da na Najeriya sun kashe wani babban dan kungiyar IS.

Hakan na zuwa ne bayan shafe watanni da sojojin Amurka suka yi a Najeriya da sunan za su taimaki kasar da yaki da ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

“Ba tare da kashe kowa ba”; Obama ya fadi yadda ya kulla yarjejeniya da Iran

Shugaba Donald TrumpShugaban Amurka, Donald Trump na bayani. Hoto: Getty Images
Source: FacebookTrump ya kashe dan ta’adda a Najeriya

A sakon da White House ta wallafa a X, ta ce Abu Bilal yana cikin manyan ‘yan kungiyar IS na duniya.

“Ba zai sake addabar mutanen Afirka ko taimakawa wajen shirya hare-haren da za su kai hari kan Amurkawa ba,”

In ji Trump.

Shugaban Amurkan ya ce kawar da al-Minuki ya sa ayyukan kungiyar IS na duniya “sun ragu matuka.”

Trump ya nuna godiya ga gwamnatin Najeriya saboda hadin gwiwar da ta bayar a samamen da aka kashe al-Minuki.

Asali: Legit.ng

Add a comment

Leave a Reply