Amurka Ta kai Hari kan Jiragen Iran, Dakarun Trump Sun Kashe Mutane

Amurka Ta kai Hari kan Jiragen Iran, Dakarun Trump Sun Kashe Mutane

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin kasar Amurka sun kai hari kan wasu jiragen ruwa da suka nufi Iran a kusa da mashigar HormuzGwamnatin Iran ta tabbatar da kai harin, inda ta ce an kashe wasu daga cikin fararen hula da ke cikin jirgin ba tare da sun aikata laifi baHakan na zuwa ne yayin da lamura ke kara zafi tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya, musamman kan mashigar ruwan Hormuz

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran – Wata majiyar soja ta ce Amurka ta kai hari kan wasu ƙananan jiragen ruwa biyu na daukar kaya na fararen hula da ke kan hanyarsu daga gabar tekun Oman zuwa gabar Iran.

Rahotannin da suka fito daga gwamnatin Iran sun nuna cewa lamarin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyar da ke cikin jiragen.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Shugaba Donald Trump da mashigar HormuzDonald Trump a hagu da mashigar Hormuz a dama. Hoto: Getty Images
Source: UGCHarin Amurka kan jiragen Iran

Rahoton Merhr News ya ce majiyar ta karyata zargin da Amurka ta yi cewa ta kai hari kan jiragen ruwan rundunar IRGC, tana mai cewa:

“Maimakon kai hari kan jiragen IRGC, Amurka ta aikata mummunan laifi ta hanyar bude wuta kan wasu kananan jiragen dauke da kayan fararen hula.”

Ta kara da cewa bayan bayanin da Washington ta fitar, an tuntubi majiyoyin yankin domin tabbatar da hakikanin abin da ya faru, ganin cewa babu wani jirgin yakin IRGC da aka kai wa hari.

“Bincike ya nuna cewa a zahiri dakarun Amurka ne suka kai hari kan kananan jiragen kaya guda biyu na fararen hula. “Jiragen suna kan hanyarsu daga garin Khasab da ke gabar Oman zuwa gabar Iran. Harin ya yi sanadin mutuwar fasinjoji fararen hula guda biyar,”

In ji majiyar.

Matsayar Iran kan harin Amurka

Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa majiyar ta jaddada cewa dole ne a daurawa Amurka alhakin laifin kashe fararen hula ba tare da laifi ba.

Kara karanta wannan

Iran ta kai farmaki kan jirgin ruwan Amurka a kusa da mashigar Hormuz

Ta danganta wannan hari da yadda Amurka ke aikata abubuwa cikin gaggawa da rashin tsari, sakamakon tsoro da firgici da ta ke ciki tun bayan gargadin da Iran ta yi kan jiragen ruwa masu shiga yankin Tekun Farisa da mashigar Hormuz.

An dade ana samun tashin hankali a yankin Tekun Farisa da mashigar Hormuz tun ranar 28 ga Fabrairun 2026, lokacin da Amurka da Isra’ila suka fara hari kan Iran ba tare da wani dalili ba.

Yadda mashigar Hormuz da ke Iran ya ke.Daya daga cikin wuraren da ake bi a wuce ta mashigar Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yanzu Iran na dagewa kan ci gaba da rike ikon mashigar Hormuz tare da karbar kudin wucewa a matsayin diyya kan barnar da Amurka da Isra’ila suka yi mata.

An kai hari matatar mai a UAE

A wani rahoton, kun ji cewa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ce Iran ta kai hari da jirgi marar matuki kan daya daga cikin tankokin man ta.

Mahukuntan UAE sun ce hare-haren sun haddasa babbar gobara a wata muhimmiyar matatar mai a yankin Fujairah da ke gabashin kasar.

Sai dai a martanin da gwamnatin kasar Iran ta yi, ta bayyana cewa bata da hannu a harin, tare da cewa Amurka za a zarga da lamarin.

Asali: Legit.ng

Add a comment

Leave a Reply