Donald Trump

Asalin hoton, AFP

10 Satumba 2025

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce yana matukar bakin ciki ta kowa ne bangare na harin da Isra’ila ta kai kan mambobin Hamas a Qatar.

Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi takaitacce ga manema labarai a Washington.

To amma tun da farko ya bayyana cewa Isra’ila ba ta sanar da shi harin ba a kan lokaci ta yadda zai gargadi Qatar din har lokaci ya kure.

Shugaba Trump ya ce ya samu bayani game da harin ne daga sojojin kasarsa a daidai lokacin da ake shirin kai harin , kodayake lokaci da tsarin harin sanar da Amurkar, har yanzu ba a san yadda yake ba.

Kusan sojojin Amurka dubu 10 na jibge a wani sansanin sojin sama da ke wajen babban birnin kasar ta Qatar, Doha, inda Mista Trump ya ce abin takaici aka kai harin.

Ya yi magana a lokacin da ya je wani gidan cin abinci a Washington.

Ya ce: ”Ba yanayi ba ne mai kyau amma zan ce muna son dawo da wadanda aka yi garkuwa da su, to amma ba ma farin ciki a kan yadda ya kasance a yau.”

Yayin da Isra’ila ta kare harin da cewa abu ne da ya dace ita kuwa Qatar cewa ta yi Israila ta ci amana kuma tana aikata ta’addanci.

Firaministan Qatar din Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya ce hare-haren na baranazar durkusar da tattaunawar zaman lafiya da Qatar din ke shiga tsakani tsakanin Hamas da Isra’ilar.

Sakatariyar yada labarai ta Shugaban Karoline Leavitt ta bayyana rashin amincewar Trump din ta Isra’ila ta yi gaban kanta wajen kai harin.

Tana mai cewa, yin gaban kai a kai harin bam cikin Qatar, kasa mai cin gashin kanta kuma kawar kut da kut ta Amurka da ke aiki tukuru tare da kasadar yin haka da Amurka don wanzar da zaman lafiya, hakan ba alheri ba ne ga muradun Isra’ila ko Amurka ba.

Sai dai kuma shugaban na Amurka ya yi bakin-ganga inda ya ce kawar da Hamas wadda ta ci moriyar akubar da wadanda ke zaune a Gaza ke sha abu ne da ya dace.

A wani sako da ya sanya a shafinsa na Sada Zumunta – Truth Social, Trump ya ce lokacin da ya samu labarin harin nan da nan ya umarci jakadansa na musamma Steve Witkoff ya gaggauta sanar da shugabannin Qatar a kan harin da ke tafe – to amma ina bakin alkalami ya riga ya bushe ba za a iya dakatar da harin ba.

Hamas ta ce ba a kashe shugabanninta da Isra’ila ta kai wa harin ba, amma ya kashe wasu mutum shida.

Write A Comment