Shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, WHITE HOUSE

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Donald TrumpBayani kan maƙalaMarubuci, Christal Hayes ,

Sa’o’i 4 da suka wuce

Shugaban Amurka Donald Trump ya shigar da BBC ƙara a kotu inda yake neman a biya shi diyyar kuɗi dala biliyan biyar, wato kwatankwacin naira tiriliyan 7,265,798,622,555, kan wani rahoto na musamman da kafar ta yaɗa game da jawabinsa na ranar 6 ga watan Janairun 2021.

Trump na zargin BBC da ɓata suna da karya ƙa’idar aiki, kamar yadda bayanan ƙarar da ya shigar a jihar Florida suka nuna.

BBC ta nemi afuwar Trump a watan da ya gabata, sai dai ta yi watsi da batun biyan diyya da kuma zargin cewa rahoton “ya ɓata sunan” shugaban ƙasar.

Lauyoyin Trump na zargin BBC da ɓata masa suna ta hanyar “yanke bayanin da ya yi da mummunar manufa”.

Ci gaba da karantawa

Har yanzu BBC ba ta mayar da martani kan ƙarar ba.

A watan da ya gabata ne Trump ya sanar da shirinsa na maka BBC kotu kan rahoton na musamman, wanda aka nuna a talabijin gabanin zaɓen shugaban Amurka na 2024.

BBC ta ce babu hujjar cewa rahoton ya cutar da Trump kasancewar an sake zaɓen shi a matsayin shugaban ƙasa jim kaɗan bayan rahoton.

“Ina ganin wajibi ne gare ni,” kamar yadda Trump ya shaida wa ƴan jarida a lokacin da yake bayar da tabbacin cewa zai shigar da ƙarar.

“Sun yi cuta. Sun sauya abin da na faɗa.”

A cikin jawabinsa ranar 6 ga watan Janairun 2021, gabanin zanga-zangar da magoya bayansa suka yi a harabar ginin majalisar dokokin Amurka na Capitol, Trump ya shaida wa magoya bayansa cewa: “Za mu yi tattaki zuwa ginin Capitol, kuma za mu yaba wa jajirtattun sanatocinmu da ƴan majalisa maza da mata.”

A can gaba cikin jawabin, tsawon tazarar kimanin minti 50, Trump ya ce: “Kuma za mu yi fada. Za mu yi faɗa kamar babu gobe.”

A shirin BBC na Panorama, wanda a cikinsa ne aka saka rahoton, an nuna Trump na cewa: “Za mu yi tattaki zuwa ginin Capitol… kuma zan kasance tare da ku. Za mu yi fada. Za mu yi faɗa kamar ba gobe.”

BBC ta amince cewa yadda aka yanka bidiyon ya “sauya ma’anar bayanin” inda ya nuna tamkar ya yi “kira ne kai tsaye cewa a tayar da hankali”, sai dai BBC ba ta amince cewa akwai batun ɓata suna ba.

A watan Nuwamba, wata takardar saƙo a tsakanin ma’aikatan BBC ta soki yadda aka yanke bidiyon, lamarin da ya yi sanadiyyar ajiye aikin shugaban BBC Tim Davie da shugabar sashen labarai, Deborah Turness.

Gabanin Trump ya shigar da ƙara, lauyoyin BBC sun mayar masa da dogon martani game da zarge-zargen nasa.

Sun ce babu mummunar manufa wajen yanka bidiyon sannan kuma hakan bai cutar da shi ba.

Sun kuma ce dama BBC ba ta da ƴancin yaɗa shirin a Amurka, saboda haka ba ta yaɗa shirin na Panorama ba a tashoshinta da ake gani a Amurka.

Duk da cewa akwai bidiyon a shafin BBC na iPlayer, waɗanda ke zaune a Birtaniya ne kaɗai za su iya kallo.

A cikin ƙarar da ya shigar, Trump ya kafa hujja da yarjejeniyar da BBC ta shiga da wasu kafafen da ke yada shirye-shiryenta, musamman wata kafa da ake zargin tana da lasisin yaɗa shirin a ƙasashen waje. BBC ba ta ce komai ba game da batun kamfanin.

Haka nan ƙarar ta yi zargin cewa akwai yiwuwar mutane a jihar Florida ta Amurka sun kalli shirin ta amfani da ɓarauniyar hanya, wato VPN ko kuma shafin BritBox.

Write A Comment