...

Asalin hoton, Tinubu/X

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ayyuka da manufofin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce za su ɗora a kan inda ya tsaya.

Shugaba Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin ƙaddamar da littafin tarihin Buhari da Dr Charles Omole ya rubuta.

Tinubu ya ce mafi girman girmamawa da za a yi wa Buhari ita ce ci gaba da ayyuakan shugabancinsa daga inda ya tsaya.

Ya bayyana cewa littafin ya nuna tarihin Buhari cikin adalci, yana bayani kan nasarori da kuma kura-kurai, tare da ƙarfafa shugabanni na gaba su koyi darussa daga rayuwar marigayin.

Shugaban ƙasar ya kuma waiwayi doguwar tafiyarsa ta siyasa tare da Buhari, inda ya bayyana shi “A matsayin ɗan’uwa da aboki da abokin tafiya a siyasa.”

Ya ce “Mun gina babbar haɗaka ta siyasa wadda ta kai ga nasarar zaben 2015, inda aka kayar da shugaban ƙasa mai ci a lokacin, lamarin da ya sauya yanayin siyasar Najeriya.”

Tinubu ya jaddada cewa haɗin kai a siyasa ba rauni ba ne, illa hikima wajen gina ƙasa.

A wajen taron, gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yabawa Shugaba Tinubu kan tsayawa tare da iyalan Buhari da kuma jihar Katsina, yana mai bayyana Buhari a matsayin mutum mai ladabi da kishin ƙasa da shugabanci nagari.

Marubucin littafin, Dr Charles Omole, ya ce littafin ya tattaro tarihin rayuwar Buhari tun daga haihuwa har zuwa rasuwarsa, tare da shaidu daga mutanen da suka yi aiki tare da shi.

Write A Comment